Shugaban Najeriya na ziyarar aiki a Kamaru | Labarai | DW | 29.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Najeriya na ziyarar aiki a Kamaru

Buhari na Kamaru ne domin tattaunawa da takwaransa Paul Biya kan yadda za su kalubalanci matsalar Boko Haram da ta addabi yankin.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya isa Kamaru da ke makwabtaka domin tattaunawa da magabatan kasar kan yadda za su hada karfi da karfe wajen kalubalantar barazanar mayakan Boko Haram da suka addabi yankin.

Bayan hare-haren kunar bakin wake guda biyar da ya haddasa asarar rayukan mutane da dama a yankin arewacin kasar, an tsarara matakan tsaro gabanin ziyarar tasa. An girke sojoji a saman gidaje da kuma a kan titin da ya kama daga filin saukar jiragen sama zuwa fadar gwamnati da ke Yaounde, daura da motocin suloke dake sintiri a dukkan titunan birnin, musamman a kewayen hotel din da aka sauke shugaban na Najeriya.

Kasashen yankin Tafkin na Chadi da suka hadar da Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da kuma Benin, sun kafa wata runduna wacce za ta shawo kan rashin tsaro da ke addabar yankin bakin daya.