1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: 'Yan sanda na binciken Bukola Saraki

Abdourahamane Hassane
June 3, 2018

A Najeriya hukumar 'yan sanda ta gayyaci shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki domin ya amsa tambayoyi a game da zargi da wani dan fashin da makami ya yi masa cewar shi ke ba su umarni.

https://p.dw.com/p/2ysLC
Nigeria Bukola Saraki
Sanata Bukola Saraki kakakin majalisar dattawan NajeriyaHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

'Yan Fashin sun ce shugaban majalisar dattijai shi ne ke ba su makamai da motoci da kuma gwamna Jihar Kwara Alhaji Abdulfatah Ahmed saboda kai hare-hare a kan jama'ar da suke kwace musu dukiyoyinsu wanda a ciki aka kashe mutane 33. Daga shekara ta 2003 zuwa 2011 Bukola Saraki ya rike matsayin gwamnan Jihar Kwara inda a ciki watan Afrilun da ya gabata 'yan fashin da makami suka fasa wani bankin.