Shugaban kasar Faransa na ziyara a Amirka kan batun tsaro | Labarai | DW | 24.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban kasar Faransa na ziyara a Amirka kan batun tsaro

Francois Hollande na Faransa ya isa fadar White House ta Amiraka a ziyarar da yake yi don tattauna yiwuwar yadda za su bullo wa batun kungiyar IS da Shugaba Barack Obama.

Wannan ziyarar Shugaba Francois Hollande dai na daya daga cikin jerin tattaunawar da yake da shugabanin duniya kan hada hannu don dakile harkokin kungiyoyin 'yan ta'adda a duniya.

Duk shugabanin dai sun yi ikirarin za su murkushe kungiyar IS da ke kawo barazana ga duniya baki daya.

Kazalika Shugaba Hollande zai yi irin wannan ganawar da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a birnin Paris a ranar Larabar nan, sannan daga bisani ya gana da Vladimir Putin na Rasha da za ta kasance a ranar Alhamis kafin ya tarbi Shugaban kasar China Xi Jinping a Paris a ranar Lahadi.