Shugaban China na ziyara a Birtaniya | Labarai | DW | 20.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban China na ziyara a Birtaniya

Shugaba Xi Jinping zai gana da sarauniya Elizabeth ta biyu a fadar Buckingham inda aka tsara masa walimar ban girma. Sannan zai ziyarci Firaministaa David Cameron.

Shugaban kasar China Xi Jinping ya fara wata ziyarar aiki ta kwanaki hudu mai cike da tarihi a Birtaniya inda ya samu wata gagarumar tarba ta alfarma irin ta sarauta. Xi Jinping zai gana da Sarauniya Elizabeth ta biyu a fadar Buckingham inda aka tsara masa wata walimar ban girma. Sannan zai ziyarci Downing Street inda zai gana da Firayiminista David Cameron, kafin ya yi jawabi a gaban taron 'yan majalisar dokokin Birtaniya. Zai dauki lokaci kan tattaunawa a abubuwa da suka shafi kasuwanci.

A cewar ofishin Cameron a wannan ziyara za a kulla harkoki na kasuwanci da zuba jari da zai lashe sama da Fam miliyan dubu 30 abin da zai yi sanadi na samun ayyuka sama da 3,900.