Shugaban Amurka na ci gaba da ziyara a Latin Amurka | Labarai | DW | 12.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Amurka na ci gaba da ziyara a Latin Amurka

Shugaban kasar Amurka G. Bush ya isa kasar Guatamala bayan ziyarar saoi 6 a kasar Colombia a rangadinsa na kasashe 5 na Latin Amurka.

A ziyarasa zuwa Bagota na kasar Colombia duk da tsauraran matakan tsaro da aka dauka,masu zanga zanga sun kona tutocin Amurka tare da fasa tagogin wasu ofisoshi suna masu nuna adawarsu ga ziyarar ta Bush,hakazalika masu zanga zanga a Brazil da Uraguay sun kara da yan sanda a lokacinda suke Allah wadai da ziyarar ta Bush.

Ana tsammanin samun zanga zangar a yau a Guatamala da kuma nan gaba a Mexico.