Shugaban Afirka ta Kudu ya yi tir da hari kan baki | Labarai | DW | 24.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Afirka ta Kudu ya yi tir da hari kan baki

Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu ya yi tir da hari kan baki 'yan Afirka cikin kasarsa lamarin da ya fara janyo zaman zullumi kan martani wasu kasashe.

Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu ya yi tir da harin da aka kai kan bakin 'yan kasashen Afirka. Ofishin shugaban ya fitar da sanarwa a wannan Jumma'a.

Kimanin shaguna 20 aka lalata a birnin Pretoria sakamakon tashin hankali na kin jinin bakin 'yan kasashen Afirka da ake zargi sun kwace aiki ga 'yan kasa. Shugaba Zuma ya ce galibin bakin suna bayar da taimakon bunkasa tattalin arzikin kasra ta Afirka ta Kudu. Bisa fusata an kai hari kan ofishin kamfanin sadarwa na MTN a birnin Abuja na Najeriya, saboda abin da ya faru na hari kan 'yan Najeriya a Afirka ta Kudu.