Shugaba Zuma na fuskantar barazana | Labarai | DW | 07.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Zuma na fuskantar barazana

Dambarwar siyasar kasar Afirka ta Kudu na ci gaba da kara dumi sakamakon kiraye-kirayen da shugaba Jacob Zuma ke sha na sai lallai ya yi murabus daga matsayinsa na shugaban kasa.

Südafrikanischer Präsident Jacob Zuma (Getty Images/S.Maina)

Shugaba Jacob Zuma na kasar Afirka ta Kudu

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma, ya dage jawabin da ya yi alkawarin yi wa al'umar kasar a jiya Talata, saboda fargabar fuskanta turjiya daga wasu 'yan majalisun kasar. Matakin dage jawabin na Mr. Zuma dai, bayanai sun ce an dauke shi bayan wata ganawar da manyan jiga-jigan jam'iyyarsa ta ANC mai mulkin kasar suka yi gabanin kuma wani babban zama na majalisar gudanarwar kasar.

Dama dai shugaba Jacob Zuma na fuskantar suka da ma kiraye-kiraye kan lallai sai ya yi murabus daga matsayinsa na shugaban kasa. Ana kuma sa ran zaman majalisar gudanarwar kasar wacce ke da ikon shirya wa shugaban kiranye, za ta yi zama a yau Laraba.