1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Buhari ya bukaci kwantar da hankula

Abdullahi Tanko Bala
August 30, 2021

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga dukkan al'umomi su hada kai su kuma kwantar da hankula bayan wani tashin hankali da ya faru a garin Jos da ya yi sanadiyar mutuwar gomman mutane.

https://p.dw.com/p/3zhQD
Muhammadu Buhari, Präsident von Nigeria
Hoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Garin Jos da ke Jihar Filato a baya ya yi fama da rikice-rikice tsakanin a'umomin Musulmi da na Kirista ko da yake jami'ai sun ce rikicin baya bayan nan ayyuka ne na 'yan ta'adda amma ba shi da nasaba da addini.

Fadar shugaban kasar ta tabbatar wa dukkan 'yan kasa cewa tana dukkan bakin kokari kuma za ta yi maganin wadanda ke aikata wannan danyen aiki.

Hukumomi a Jihar Filaton dai sun kafa dokar ta baci na sao'i 24 a birnin Jos da kewaye kafin daga bisani a sassauta a wannan Litinin inda aka mayar da dokar daga karfe 6:00 PM na yamma zuwa 6:00 AM na safe.

Dukkan bangarori na shugabannin Fulani musulmi da na Kirista sun musanta cewa jama'arsu na cikin wadanda suka kai hare haren.