Shugaba Al-Assad na Syria yayi tazarce
May 29, 2007Talla
Opishin ministan cikin gida na ƙasar Syria, ya bayyana sakamakon zaɓen da jama´ar ƙasa ta gudanar a jiya lahadi.
Wannan sakamako ya nunar da cewa, kashi kussan 98 cikin ɗari na jama´ar da su ka kaɗa ƙuri´ a ,sun nuna amincewa da shugaban ƙasa Bashar Al –Assad, ya yi tazarce , har tsawan shekaru 7 masu zuwa.
Ministan cikin gida, Bassam Abdel Madjid, ya nuna gamsuwa da wannan sakamako, da ya dangata da ci gaban demokradiyar a Syria.
A watan da mu ke ciki ne, yan majalisar dokoki su ka buƙaci Bashar Al-ASssad, ɗan shekaru 41 a dunia, ya sake ajje takara.
An zaɓe shi da farko a shekara ta 2000,domin ya gaji uban sa, Hafez El Assad da Allah ya ma cikawa.