1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici na dakile armashin yakin neman zaben Kamaru

Mouhamadou Awal Balarabe SB
February 7, 2020

Tagwayen zabukan kananan hukumomi da na majalisar dokokin Kamaru. Sai dai kaurace wa zabukan da babbar jam'iyyar adawa ta MRC ta yi da kuma rikice-rikicen da ake fama da su a yankin Ingilishi sun rage wa zaben armashi.

https://p.dw.com/p/3XPTp
Kamerun Präsidentschaftswahlen Unterstützer von Maurice Kamto
Hoto: Reuters/Z. Bensemra

A mafi yawancin kananan hukumomi 360 da Kamaru ta kunsa, 'yan takara na gangamin yakin neman zabe tare da zuwa gida-gida domin zawarcin kuri'un 'yan kasa. Amma a yankin Ingilishi da ya kunshi kananan hukumomi 65, harkokin na siyasa na tafiyar hawainiya sakamakon kalubalen tsaro da ake fuskanta. In banda babban gangami da jam'iyyar CPDM da ke mulki ta gudanar a Bamenda, babu yakin neman zaben a zo a gani da sauran jam'iyyu ke yi. Hamidou Mohd mazaunin garin Bamenda ya ce Wannan kuwa ba ya rasa nasaba da barazanar da 'yan aware suka yi na far ma wadanda suka shiga aka dama da su a harkokin zabe.

Präsidentschaftswahl in Kamerun Straßenszene in Douala
Hoto: DW/F. Muvunyi

Jam'iyyar RDPC/CPDM da ke mulki ta mamaye yakin neman zabe saboda akwai wasu mazabu na kasar da ba ta da abokan hammaya imma a zabukan kananan hukumomi ko na 'yan majalisar dokoki. Amma kuma bai hana 'yan takarar bangaren da ke mulki yin dar-dar a Maroua da kewaye sakamakon tabarbarwar harkokin tsaro a lokacin da suke gudanar da yakin neman zabe ba.

Fiye da jam'iyyu siyasa 30 suka tsayar da 'yan takara a mazabu dabam-dabam na Kamaru domin samun kujera a majalisar dokokin kasar mai wakilai 180. Sai dai babbar jam'iyyar adawa ta MRC ta kaurace wa zabukan saboda tana ganin cewar bai dace a gudanar da zabukan a cikin yanayi na hare-haren ta'addaci da kuma rikicin aware a yankin Ingilishi ba. Amma Albert Elimbi Lobé, manazarcin harkokin siyasa ya ce  jam'iyyar MRC ta Maurice Kamto ba burma wa kanta wuka domin ba za ta iya shiga zaben shugaban kasa mai zuwa ba.

Der kamerunische Oppositionspolitiker Maurice Kamto spricht am 30. Januar 2019 in Paris vor den Medien
Maurice Kamto jagoran 'yan adawa a kasar KamaruHoto: DW/M. Mefo

"Akwai ka'idoji da ya kamata a cika don a shiga zaben. Misali, kafin MRC ta sami damar tsayar da dan takara a zaben shugaban kasa mai zuwa, wato a shekarar 2025, dole ne ta samu 'yan majalisa biyu, abin da ba zai samu ba. Saboda haka a shekarar 2025, Jam'iyyar ba za ta iya tsayar da dan takarar shugaban kasa ba."

Ya zuwa yanzu 'yan takara da jam'iyyun siyasa ba su sami tallafin yakin neman zabe daga gwamnati ba kamar yadda doka da tanada, lamarin da ya suke sara suna duban bakin gatari a lokacin da suke fitar da kudin.