Ana son shirya gasar cin kofin duniya bayan duk shekaru biyu
September 20, 2021Za mu fara da batun taron da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ke shirin gudanarwa dangane da batun yiwuwar shirya gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya duk bayan shekaru biyu maimakon shekaru hudu da ake yin gasar a yanzu. Ana dai sa ran hukumar ta FIFA za ta gudanar da taron ta kafar Internet da dukkanin masu ruwa da tsaki a fannin kmwallon kafa, a ranar 30 ga wannan wata na Satumba da muke ciki. Wannan batu dai ya janyo cece-kuce musamman daga kasashe Turai, inda shugaban Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta nahiyar Turai UEFA Aleksander Ceferin barazanar janyewa daga gasar ta cin kofin kwallon kafa na duniya. Ita ma dai Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta kasar Jamus DFB ta nuna rashin jin dadinta da wannan yunkuri.
Matsayin Ghana ya bar baya da kura
Bayan da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniyar FIFA ta ayyana kasar Gahan a matsayin ta 53 a fannin kwallon kafa a duniya, hankula sun tashi kuma rayuka sun baci a kasar ta Ghana abin da ya kai ga korar mai horasa da 'yan kungiyar wasan kwallon kafa ta kasa wato Black Stars. Hukumar Kwallon Kafa ta Ghana ce dai ta bayyana wannan mataki, sai dai har ya zuwa wannan Litinin din ba a kai ga sanin waye zai gaje shi ba, duk kuwa da rade-radin dawo da tsohon mai horas da 'yan kungiyar ta Black Stars ta Ghana. Ga dai wakiliyarmu ta Accra Jamila Ibrahim Maizango dauke da kariun bayani.
Halin da ake ciki a kakar Bundesligar Jamus
A karshen mako aka ci gaba da fafatawa a kakar lig-lig ta Jamus wato Bundesliga, inda a ranar Jumma'ar da ta gabata Herthe Berlin ta lallasa kungiyar kwallon kafa ta Fürth da ci biyu da daya. A wasannin da aka gudanar ranar Asabar kuwa, an tashai wasa babu ci tsakanin Hoffenhedim da Arminia Bielefeld, haka kuma abin yake tsakanin Mainz da Freiburg. Borussia Mönschengladbach ta sha kashi a hannun Augsburg da ci daya mai ban haushi an kuma tashi wasa kunnen doki daya da daya a wasan da aka kara tsakanin Cologne da Rb Leipzig. Sai wasan da aka yi ruwan kwallaye, wanda da ma ana iya cewa karfin ba daya ba, wato wasa tsakanin FC Bayern Munich da VfL Bochum da ta shigo rukuni na daya na Bundesligar a bana. An dai tashai wannan wasa Bayern na da ci bakwai Bochum na nema. Kuma wannan wasan ne ma sashen Hausa na DW ya kawo muku kai tsaye a ranar Asabar din karshen mako.
A wasannin da aka kara a jiya Lahadi kuwa, Borussia Dortmund ta lallasa Union Berlin da ci hudu da biyu kana an tashi wasa kunnen doki daya da daya tsakanin Eintracht Frankfurt da Wolfsburg, ita kuwa Leverkusen ta bi Stuttgart har gida tare da caskara ta da ci uku da daya. A yanzu haka dai, Bayern ke saman tebur da maki 13 yayin da Wolfsburg ke biye mata a matsayi na biyu ita ma da maki 13 sai kuma Borussia Dortmund a matsayi na uku da maki 12 kana Leverkusen a matsyi na hudu da maki 10 sai Mainz a matsayi na biyar ita ma da maki 10.
Mu leka a gasar Premier League
An tashi wasa tsakanin Manchester City da Southhampton babu ci kana Leverpool ta lallasa Crystal Palace da ci uku da nema haka ma Asatonvilla ta lallasa Everton da ci uku da nema. Ita ma dai Manchester United ta samu galaba a kan West Ham da ci biyu da daya kana Chelsea ta lallasa Tottenham da ci uku da nema. A yanzu haka dai Chelsea ce ke a matsayi na daya a teburin kakar ta bana da maki 13, yayin da Leverpool da Manchester United ke biye mata a matsayi na biyu da na uku da maki 13 suma kowaccensu.
Dan tseren keken nan Filippo Ganna ya sake samun nasarar lashe gasar tseren keke ta gwaji da aka gudanar a kasar Beljiyam. Ganna ya lashe tseren farko na cin kofin Flanders championships na tsawon kilomita sama da 43, cikin mintuna 47 da dakika 48 yayin da Wout van Aert ya zo na biyu da karin dakika biyar kacal kana Remco Evenepoel ya zo na uku. Shi kuwa Tadej Pogacar sdan kasar Slovenia da ya lashe gasar Tour de France har sau biyu, ya kammala gasar a wannan karo a matsayin na 10.