Cikin shirin za a ji yadda take sama tana dabo a Kamaru dangane da neman sulhu tsakanin gwamnati da 'yan awaren kasar na yankin nan mai amfani da turancin Ingilishi. Wasu kalaman Shugaba Issoufou Mahamadou na Jamhuriyar Nijar a kan matsayin birnin Kidal na kasar Mali sun janyo cece-kuce.