Shirin tsarin iyali a Indiya ya janyo asarar rayuka | Labarai | DW | 11.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin tsarin iyali a Indiya ya janyo asarar rayuka

Sama da mata 60 suka jikkata wasu kuma tuni suka rasu bayan wani shirin ƙayyade iyali a Indiya.

A ƙasar Indiya, aƙalla mata 10 suka mutu wasu da dama na fama da rashin lafiya, bayan bin wani tsarin ƙayyade iyali wanda gwamnati ƙasar ta fitar. Gwamnatin Indiya wadda ke ta biyu a yawan jama'a duniya, tana bin wani tsari na yi wa mata tiyata, domin neman hanyar rage bunƙasar da jama'a ke yi a ƙasar. Yanzu haka dai mata sama da 60 ke fama da rashin lafiya, bayan an yi musu wannan fiɗar.