Shirin tsagaita wuta a Siriya na cikin hadarin rugujewa | Siyasa | DW | 29.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shirin tsagaita wuta a Siriya na cikin hadarin rugujewa

Manyan kasashen duniya na ci gaba da nuna fata kan dorewar yarjejeniyar tsagaita wuta a Siriya tsakanin bangarorin da ke rikici wadda take tangal-tangal.

Tuni bangarorin da ke yaki da juna a Siriya suka fara zargin juna da karya yarjejeniyar tsagaita wutar wadda ta fara aiki a karshen mako, duk da matsalolin da ake samu a wasu wurare. Yarjejeniyar da ke zama mai inganci karo na farko cikin shekaru biyar da kasar ta Siriya ta kwashe cikin rikici, kuma duk da matsaloli yarjejeniyar tsagaita wutar ta yi tasiri.

Ministan harkokin wajen kasar Jamus, Frank-Walter Steinmeier ya nuna fata bisa ganin amfani da damar yarjejeniyar domin samun mafita ta siyasa:

"Ga abin da yake faruwa za a ci gaba da aiki da yarjejeniyar idan aka samu tsari na siyasa, wanda zai canja siyasar Siriya. Kuma na yi farin ciki da manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya, Staffan de Mistura wanda ya ce zai gayyato bangarorin siyasa na kasar da suka hada da wakilan gwamnati, da 'yan adawa zuwa birnin Geneva domin tattaunawa a watan Maris. Ina fata haka zai dore."

Kai agaji ga wadanda aka yi wa kawanya

Bisa yarjejniyar Shugaba Bashar al-Assad na Siriya da masu adawa da gwamnatinsa sun amince da tsagaita wutar idan ma'aikatan jinkai za su yi amfani da damar wajen kai wa ga dubban mutane. Yakin basasar na Siriya ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane 250,000 sannan wasu fiye da miliyan 11 suka rasa gidajensu.

Sai dai kasashe irin su Saudiya suna nuna tantama bisa dorewar yarjejniyar, kamar yadda ministan harkokin wajen kasar Adel Al-Jubeir ke cewa:

"Idan ba za mu ci gaba da aiki da yarjejeniyar ba, akwai wani zabin kamar yadda John Kerry ya fada. Akwai wani shiri, idan babu aiwatarwa daga bangaren gwamnatin Siriya da masu mara mata baya, za mu mayar da hankali kan wata mafitar."

Ministan harkokin wajen kasar ta Saudiya Adel Al-Jubeir ya kuma fito fili ya zargi dakarun sama na Rasha da karya yarjejeniyar.

Sulhu na siyasa shi ne mafi a'ala

Ministan harkokin wajen Denmark Kristian Jensen ya jaddada wannan magana idan ya ce gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad ba ta da wani muradi mai kyau:

"Mafita ta siyasa ce kawai bisa rikicin Siriya, da yakin basasa, amma mafita ta siyasa tana hade da barazana na karfin soji, idan ba haka ba Assad zai ci gaba da aikin jahilci inda gwamnati ta hallaka dubban mutanenta, sannan rabin al'uma suka zama 'yan gudun hijira."

Kwakkaran mataki da yadda za a tunkarin abin da ke faruwa a Siriya bisa zargin juna da karya yarjejeniyar zaman lafiya su ne za su tantance makomar al'umar kasar.

Sauti da bidiyo akan labarin