Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Za a ji yadda rikicin siyasar Mali da Najeriya suka zama batutuwan da suka dauki hankali a mako mai karewa
Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO na kara daukar mataki a kan yawaitar juyin mulki da sojoji ke yi a yanki.
A kasashen Afirka da dama, 'yan jarida na fuskantar barazana ta kowace fuska mussaman a kasashen Kamaru da Guinea-Bissau da Ruwanda da kuma Mali da ke karkashin mulkin soja.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga sojoji a kasashen Burkina Faso da Guinea da kuma Mali da su mayar da shugabancin kasar hannun fararen hula.
A birnin Accra na kasar Ghana, shugabannin kasashe membobin kungiyar ECOWAS na halartar taron koli kan batun juye-juyen mulkin da aka yi a wasu kasashe uku na yammacin Afirka.