A cikin shirin za a ji cewa a daidai lokacin da ake yakin neman zabe a kasar Chadi matasa da dama ne ke korafi da rashin aikin yi, a yayin da Kungiyar Reporters sans frontières ta bukaci a sako tsohon daraktan rediyo da talabijin CRTV da aka damke a Kamaru.