Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A cikin shirin bayan kun sha Labaran Duniya, muna tafe da rahoto kan yadda tashin nakiyoyi ke kara jefa rayuwar al'umma cikin tasku da ma asarar rayukan a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
A wani yunkuri na zaben cike gurbi na majalisar dokoki, hukumar zaben Nijar ta fitar da jadawalin rijistar sunayen masu kada kuri'a daga kasashen ketare.
Hukumar dakile cutttuka masu yaduwa ta Najeriya ta tabbatar da cewa mutane 21 ne suka kamu da cutar Kyandar biri a kasar.
Dakarun Jamhuriyar Nijar sun yi ikirarin halaka mayakan Boko Haram 40 a wasu tsibirai na yankin Tafkin Chadi a yayin da suka yi nasarar dakile yunkurin wani mummunan hari.
Kungiyar tarayyar Turai ta bayyana bukatar kara yawan makamashin iskar gas da take saye daga Najeiya sakamakon kutsen Rasha a Ukraine da ya sanya nahiyar Turan neman hanyar cike gibin iskar gas da take saya daga Rasha.