1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin lafiya Jari: Matsalar ciwon Iskokai

Abdullahi Maidawa Kurgwi
June 21, 2019

Matsalar ciwon Iskokai matsala ce wacce ta dade tana shafar rayuwar al'umma, inda wasu lokutan matsalar kan kai ga  jirkitar da rayuwa mutane tun daga lokacin da suka sami wannan ciwo.

https://p.dw.com/p/3Kpc6

Masana dai sun lura cewar anfi fuskantar wannan matsala ta iskokai ne a kauyuka ko yankunan karkara, kuma wannan matsala ta iskokai kan samo hasali ta sanadi daban daban.

Akasarin lokuta wasu na danganta ciwon Iskokai da ciwon hauka, duk da cewar wasu kan sami kansu cikin yanayi na shaye shaye wanda kan jirkita musu kwakwalwa su rika sambatu, yayin da wasu kan shiga halin dimauta ta rayuwa sanadiyar maita ko makamantan su.