1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shirin Labarin Wasanni

Lateefa Mustapha Ja'afar AMA
May 31, 2021

Kungiyar Chelsea ta lashe gasar zakarun nahiyar Turai, a yayin da 'yan wasan Cologne suka sha da kyar a Bundesliga. Masar ta lashe wasan kwallon kwando na zakarun nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/3uEJt
Weltspiegel | 31.05.2021 | Chelsea gewinnt Champions League Finale
'Yan wasan Chelsea na murnan cin kofin zakarun TuraiHoto: David Ramos/REUTERS

Kai Havertz dan wasan baya na kungiyar Chelsea ne dai ya cirewa kungiyar tsa kitse a wuta, bayan da Havertz mai shekaru 21 a duniya dan asalin kasar Jamus ya zura kwallo a mintina na 42 da fara wasan. Wannan dai ya bai wa Chelsea damar lashe kofin na gasar zakarun Turai a karo na biyu, wato bayan ta samu nasarar lashe gaasar a 2012 da kuma wannan shekarar ta 2021. An dai tashi wannan wasa da aka fafta a kasar Portugal tsakanin Manchester City da ke zaman zakarar kwallon kafa a gasar lig-lig na kasar Ingila wato Premier lieague da kuma takwararta ta Chelsea da ke zaman ta hudu a gasar ta Premier Leag da ci daya da nema. Ita dai kungiyar kwallon kafa ta Manchester City  da ta sha kashi da ci daya mai ban haushi a hannun Chelsea, wannan ne karo na farko da ta samu kai wa ga wasan karshe, bayan da ta lallasa Brossia Dortmund ta Jamus da kuma Real Madrid ta kasar Spain a wasannin.

Fußball Porto | UEFA Champions League Finale | Trainer Thomas Tuchel
Coach Thomas Tuchel na kungiyar ChelseaHoto: Pierre P. Marcou/AFP/AP/picture alliance

Da yake jawabi bayan da suka lashe wannan gasa, mai horas da 'yan wasan na Chealsea wanda za a iya cewa ya samu wannan babbar nasara cikin watannin biyar Chelsea coach Thomas Tuchel ya nunar da cewa, da ma ya tsammaci nasara gabainn fara wasan. Tsohon mai horas da 'yan wasa na kungiyoyin Mainz da  Borussia Dortmund na Jamus da kuma Paris Saint-Germain ta Faransa Tuchel ya kara da cewa  "Babbar nasara ce, tabbas mun ji dadin kasancewarmu a wannan matsayi kuma za mu yi amfani da wannan dama a nan gaba a duniya baki daya, inda matukar farinciki a wannan lokaci, na rasa bakin magana, wannan nasararmu ce, nasara ce ga 'yan wasan nasara ce ga kowa."

Haaland ya fi kuwa zura kwallo a gasar zakarun Turai

Deutschland Bundesliga - VfL Wolfsburg v Borussia Dortmund | Tor Haaland
Haaland dan wasan da yafi yawan kwallayeHoto: Darius Simka/regios24/imago images

Wannan dai shi ne karo na biyu da Tuchel mai shekaru 47 a duniya, ke samun nasarar zuwa wasan karshe a gasar ta zakarun nahiyar Turai, bayan da ya gaza samun nasara a lokacin da ya jagoranci kungiyar Paris Saint-Germain da ta zama ta biyu a gasar ta zakarun nahiyar Turai a bara bayan da ta yi rashin nasara da ci daya da nema a wasan da suka fafata da kungiyar Bayern Munich ta Jamus. Cikin watan Disamra bara ne dai, kungiyar ta Paris Saint-Germain ta sallami Tuchel, inda kuma nan take kungiyar Chelsea ta dauke shi aiki. An dai bayyana dan wasan Brussi Dortmind Erling Haaland a matsayin dan wasan da ya fi zura kwallo a gasar ta zakarun nahiyar Turai ta bana, inda ya zura kawallaye 10 a raga. Ya dai sha gaban fitattun 'yan wasa kamar Mbappé da Neymar na kungiyar Paris Saint-Germain da ke da kwallaye takwas da shida da kuma Messi na FC Barcelona mai kawallaye biyar, yayin da  Cristiano Ronaldo na Juventus ke da kwallaye shida kacal.

Kungiyar Cologne ta sha da kyar a Bundesliga

Mai horas da 'yan wasan kwallon kafa na Jamus Joachim Loew ya yi wa 'yan wasansa biyu a karon farko cikin shekaru biyu wato Thomas Mueller da Mats Hummels domin su fafata a gasar kwallon kafa ta nahiyar Turai wato Euro 2020 a wasan da za su yi da kasar Denmark. Ita kuwa kungiyar kwallon kafa ta Cologne ta Jamus, ta sha da kyar ne bayan da ta kusa fadawa gasar Bundesliga rukuni na biyu. Kungiyar ta Cologne dai kare a matsayi na 16 a kakar wasannin Bundesliga ta bana, abin da ya tilasta mata buga wasan neman mafita tsakaninta da kungiyar Holstein Kiel da ke a matsayi na uku a rukuni na biyu na Bumndesliga. A zagayen farko na wasan dai, Cologne ta sha kaye da ci daya da nema, yayin da a karshen mako ta ceto kanta a zagaye na biyu na karawar tasu ta hanyar lallasar Holstein Kiel din da ci biyar da daya. 

CAF Super Cup 2020 in Katar ES Tunis - Zamalek
'Yan wasan Zamalek na MasarHoto: Getty Images/AFP/K. Jaafar

Kungiyar Zamalek ta zama zakarar nahiyar Afirka

'Yan wasan kwallon kwandon kasar Masar Zamalek ta zama zakarar nahiyar Afirka bayan da ta lashe kofin gasar kwallon kwando da aka yi a karon farko a Afirka.  An kirkiri wannan gasa ce da hadin gwiwar hukumar kwallon Kwandon Amirka ta NBA da kuma ta kwallon Kwando ta duniya. Kungiyoyi 12 daga nahiyar Afirka suka kara a gasar, wadanda suka hada da, Aljeriya, Angola, Kamaru, Masar, Madagascar, Mali, Morocco. Mozambique, Najeriya, Ruwanda, Senegal da kuma Tunisiya. Wannan shi ne karon farko da hukumar NBA ta kaddamar da wata gasa a wajen yankin arewacin Amurka.