1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Nijar: Shirin inganta gidan kurkuku na Koutoukale

Gazali Abdou Tasawa RGB
March 22, 2022

Gwamnatin Nijar ta kaddamar da shirin gyara tare da inganta rayuwar fursunoni da ke tsare a gidan yarin nan na Koutoukale bayan shan suka daga Kungiyar Amnesty.

https://p.dw.com/p/48rj3
Gefängnis Koutoukale im Niger
Hoto: DW/A. Mamane

A wannan Talata babbar Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta Nijar wato CNDH ta sanar da shigar da shawarwari ga gwamnatin kasar domin inganta yanayin rayuwar fursunoni na babban gidan kurkuku na Koutoukale mai tsananin tsaro. Ta sanar da hakan ne a wata fira da manema labarai, bayan sanarwar da Kungiyar Amnesty International ta fitar, inda ta nuna damuwarta kan abin da ta kira tauye hakkin dan adam da ake aikatawa a gidan kason na Koutoukale.

Kungiyar AmnestyInternational ce ta soma nuna damuwarta dangane da abin da ta kira tauye 'yancin dan adam da ake yi a gidan kason na garin Koutoukale mai tsananin tsaro da ke kunshe da ‘yan siyasa da fararen hula da sojoji da kuma ‘yan ta’adda. Kungiyar ta tayi zargin cewa, ana hana wa fursunonin 'yancin walwala kamar hanasu ziyarar iyalansu da 'yan uwansu da hana kawo musu abinci daga waje da kin ba su damar ganin lauyoyinsu da likitocinsu idan suna fama da rashin lafiya da dai sauransu matsaloli, wanda hakan ya tauye hakkin dan Adam.

Logo von Amnesty International
Amnesty ta koka da halin rayuwar fursunoni

A wata firar da kakakin hukumar ta CNDH yayi da manema labarai kan sanarwa ta Amnesty ya ce, hukumarsu ta kai ziyara a gidan kason na Koutoukale inda ta tabbatar da wasu daga cikin matsaloli. Hukumar CNDH ta ce, bayan ziyarar da ta kai ta bayar da shawarwari ga gwamnati kan inganta yanayin rayuwar 'yan kason wadanda kuma ta ce, tuni gwamnatin ta fara aiwatar da su.

Yanzu haka gwamnatin jamhuriyar Nijar ta soma wani aiki na gyaran dokokin shari’a a kasar da nufin shawo kan irin wadannan matsaloli da ake fuskanta a gidajen kurkuku da ke a sassan kasar.