Shirin Abu Namu(10.07.2019) | Zamantakewa | DW | 15.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Shirin Abu Namu(10.07.2019)

A wannan mako shirin zai duba taron da shugabannin matan Afirka suka shirya a birnin Yamai inda suka fitar da shawarwari na shawo kan kalubalan da mata ke fuskanta a rayuwa a Afirka, shawarwarin da suka gabatar wa taron AU na birnin Yamai.

Saurari sauti 09:38

Gabanin taron koli na Kungiyar AU da ya gudana a birnin Yamai  na Jamhuriyar Nijar kan batun yarjejeniyar kasuwanci maras shinge a Afirka, kungiyoyin mata da ma masu ruwa da tsaki a al'amuran matan a Afirka, sun gudanar da wani taro a kasar ta Nijar, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin matan Afirka tare da fito da shawarwari na shawon kansu, shawarwarin da kuma suka gabatar da su ga taron na AU domin a share wa matan hawayensu.