1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin Abu Namu

Ramatu Garba Baba MAB
October 8, 2018

Shirin ya duba matsalar bautar da mata da yara kanana da aka dade ana fuskanta, inda kungiyoyi da gwamnatoci suka sha alwashin daukar matakai don ganin bayanta. Sai dai ana ci gaba da fama da ita a tarayyar Najeriya.

https://p.dw.com/p/369fp
Delta Wahlkampf 2
Hoto: DW/Katrin Gänsler

Yayin da ake ci-gaba da yaki da wannan dabi'a dai, wasu kungiyoyi masu fafutuka a arewacin Najeriya sun ce sun sake bankado wani sabon salo da ake amfani da shi wajen bautar da mata da yaran mata da kuma matsalar yawaitar yi wa yara kanana fyade. A wannan karon matsalar aikatau ta kunno kai ta kuma yi kaka-gida a tsakanin ma'aurata inda aka gano yadda wasu maza suka yi musayar aikin daukar dawainiyar iyali da ya rataya a wuyansu suka aza wa matansu.

Shirin Abu Namu ya yi kokarin ji daga bakin matan da lamarin ya shafa ba tare da yin nasara ba, amma wata ganau ta bayyana halin da ire-iren matan da ake magana a kansu suka samu kansu na yin aikin aikatau kafin su ciyar da iyali.