1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ngozi Okonjo-Iweala shugabar WTO

Lateefa Mustapha Ja'afar AH
March 1, 2021

Shirin Abu Namu ya yi nazari ne kan nasarar darewa kan shugabancin kungiyar cinikayya ta duniya WTO da Ngozi Okonjo-Iweala.

https://p.dw.com/p/3q3hC
Ngozi Okonjo-Iweala | neue WTO-Chefin
Hoto: Gian Ehrenzeller/KEYSTONE/dpa/picture alliance

An zabi Ngozi Okonjo-Iweala mai shekaru 66 a duniyar, yayin taron da suka gudanar a Geneva a matsayin shugabar kungiyar ta WTO, sai dai kujerar naki da shugaban Amirka na wancan lopkaci Donald Trump ya hau ta so ta kawo mata cikas. A karshe dai ta samu nasara, bayan da abokiyar takararta daga Koriya ta Kudu ta janye kana sabon shugaban Amirka Joe Biden ya bayyana goyon bayansa ga Okonjo Iweala da ke da takardar shaidar zama 'yar Amirkan tun daga shekara ta 2019. An haifi Ngozi Okonjo-Iweala a Ogwashi-Ukwu, da ke Jihar Delta a Tarayyar Najeriya, mahaifinta Farfesa Okonjo ya kasance Obi wato sarki ke nan daga gidan sarautar Obahai a Ogwashi-Ukwu. Bayan da ta yi karatunta na firamare da sakanddare a birnin Badun, ta garzaya zuwa jami'ar Harvard inda ta kammala karatunta na digiri a fannin tsimi da tanadi a shekara ta 1976 kana ta kammala digirinta na digirgir a shekara ta 1981 a fannin tattalin arzikin yanki da ci-gaba a cibiyar fasaha ta Massachusetts. Okonjo-Iweala ta rike mukamin ministar kudi a Najeriya har sau biyu kana ta rike mukamin ministar harkokin kasashen ketare duk dai a kasarta Najeriya.