Jamhuriyar Nijar: Saukaka farashin shinkafa
January 28, 2026
A baya dai kasar ta Nijar ta sha ikirarin cewa Noma da kiwo shine babbn arzikinta, amma kuma kasar na fuskantar matsaloli na karancin abinci a kowace shekara lamarin da ya yi kamari a lokacin da aka kakaba wa kasar takunkumi sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi na ran 26 ga watan yulin 2023 kuma hakan ya koyar way an kasar babban darasi.
Manufar matakin
Burin wannan baje kolin da shugaban kasar ta Nijar janar Abdourahamane Tiani ya ayyana wanda kuma ma’aikatar kula da noman gandari ta ONAHA ta tsara tare da taimakon asusun taimakon juna na kasar ta Nijar, shi ne na kama wa manoman shinkara ta yadda za su siyar da shinkafar da suka noma cikin gaggawa sannan su samu karfin fuskantar wani sabon kaka na noman shinkafar wanda a hannu daya kuma al’umma ta kasa ta samu shinka ta gida cikin farashi mai sauki.
Hakan kuma ya samu ne bayan da kamfanin shinkafa na kasar ta Nijar ya sussuka bahunan shinkafa kimanin dubu 25 da suka fito daga gandari na manoman Tillabery da Yamai, wanda hakan ya sa aka samu kimanin ton 1000 na shinka da aka karkasa a bahu-buhu masu nauyin kg 25, 10, da kuma kg biyar. Laptanan Kanal Bilali Alhaji Gambobo shi ne babban daraktan kasa na ma’aikatar kula da noman gandari ta ONAHA, wanda shi ne aka dora wa nauyin gyaran gandari a fadin kasar kuma ya ce suna aikin domin bunkasa harkokin noma.
Kungiyoyin manoma
A fuskar hadaddiyar kungiyar nan ta mazauna karkara da ta hada manoma da makyaya na kasa baki daya wadda Djibo Bangna yake jagoranta, sun sanar cewa tun yau da shekaru da dama sun sha jan hankalin magabata na a bada cikeken goyon baya ga noma da kiwo don samun mafita daga kangin talauci:
An dai samu mutane dafifi da suka je domin sayan wannan shinkafa da manoman na Nijar suka samar inda kuma ake sayar da ita cikin farashi mai sauki bisa tallafin gwamnati duk kuwa da cewa ba kowa ne yake da kudin sayanba ganin yadda a hannu daya al’umma ke kokawa darashin kudade a hannunsu.
Wannan shinkafar dai da yanzu ake sayarwa bahu dan kg 25 a jika goma da rabi zuwa jika tara, wanda a baya an saya har jika 15 - 16 na CFA a cewar babban daraktan ma’aikatar ONAHA ta kasa, kimanin kaso 30 cikin 100 ne kawai aka fiddo na shinkafar ta yankin Yamai da Tillabery, inda a sauran jihohin kasar ta Nijar ko’ina aka tashi haikan wajen noman na shinkafa dama su alkama zuwa masara da zimmar kai wa ga tudun mun tsira na samar isheshen abinci a kasar ta Nijar. Sai dai kuma lokacin da Azumin watan Ramadan ke karatowa yan kasar ta Nijar musamman ma’aikata yan kwantragi na fatan samun dukannin albashin dasuke biyar gwamnati domin suma su ci irin wannan kasuwa.