1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Gwamnati ta kama wakilin DW Hausa

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 23, 2026

Gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar, ta cafke tare da tsare wakilin Sashen Hausa na DW a Yamai fadar gwamnatin kasar Gazali Abdou Tasawa.

https://p.dw.com/p/57Lx7
Jamhuriyar Nijar | Gazali Abdou Tasawa | DW Hausa | Tsarewa
Gazali Abdou Tasawa a gaba sanye da hula hana salla, tare da abokan aiki a DW HausaHoto: DW/P. Böll

Tun a jiya Alhamis 22 ga wannan wata na Janairu 2026 da muke ciki ne dai, jami'an 'yan sanda suka gayyaci Gazali Abdou Tasawa wakilin Sashen Hausa na DW, a Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar Nijar din zuwa ofishinsu domin amsa tambayoyi. Daga bisani sun sallame shi, amma suka bukaci ya koma da lauyansa a Jumma'a 23 ga watan na Janairun 2026, sai dai kotu ta iza keyarsa zuwa gidan kaso na Yamai, inda zai yi zaman jiran tsammanin sauraron shari' da kuma yanke hukunci. Kawo yanzu dai, babu cikakken bayani kan dalilin kamawa tare da tsare Gazali.