Shettima: Muna kokarin sake gina makarantun Borno | Siyasa | DW | 01.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shettima: Muna kokarin sake gina makarantun Borno

Gwamnan jihar Bornon Najeriya Kashin Shettima ya bayyana kokarin da suke yi na farfado da makaratu, bayan da iyaye suka bukaci gwamnati ta bai wa 'ya'yansu damar zuwa neman ilmi bayan shafe tsawon lokaci ba karatu.

Kashim Shettima Gouverneur Bono Nigeria

Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima

Kungiyar Boko Haram ta sha kai farmaki kan malamai da dalibai a makarantu, abinda ya tilasta wa gwamnati rufe makarantun. A hira ta musamman da ya yi da tashar DW, Gwamnan jihar ta Borno Kashim Shettima, ya bayyana cewa ko da yake an rufe makarantu na tsawon lokaci, amma hakan bai sa gwamnatinsa yin watsi da harkar karatu ba, inda ya ce sun dau matakan tura malamai zuwa kasashen waje don kara sanin makamar aiki, kuma a yanzu da zaman lafiya ya fara dawowa za a tura wadanan malamai a makarantun sassa daban-daban na jihar. Shettima ya kara da cewa wasu daga malaman da suka samo horo a kasashen waje za su koyar wa 'yan uwansu abinda suka koyo, wasun su kuwa za su ci gaba da zama malamai a ajujuwansu.

Rikicin Boko Haram ya yi sanadin rayukan malaman makaranta da yawa a jihar Borno, don haka a yanzu baya ga sake gina makarantu da aka lalata, gwamnatin jihar da ta Tarayya suna hada hannu don diban sabbin malaman makaranta, inda gwamnan jihar ya ce tuni suka fara hada takardun wadanda suka kammala karatun jami'a don daukarsu aikin malanta, kamar yadda gwamnatin Tarayya ta bukata.

Gwamna Kashim Shettima, ya fadawa DW cewa a yanzu haka sun bada kwangilar gina manyan makarantu tara a jihar, kana nan da watan Satumba suna saran bude daukacin makarantun da ke a jihar.

Sauti da bidiyo akan labarin