Shell zai biya diyya a Najeriya | Labarai | DW | 07.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shell zai biya diyya a Najeriya

Yanzu kamfanin na Shell mai hakar albarkatun man fetir a Najeriya ya amince zai biya al'umma da ya lalatawa muhalli a yankin Niger Delta Fam miliyan 55.

Nigeria Bodo, Ogoniland Öl

Yankin Bodo a Ogoni ta Niger Delta a Najeriya

Abin da sashin da ke lura da al'a muran da suka shafi kula da muhalli da na kare hakkin bil Adama a kungiyar Amnesty International suka bayyana da cewa nasara ce babba ga al'ummar wannan yanki.

Shekaru shida bayan wasu ayyukan na kamfanin na Shell ya tagayyara rayuwar al'ummar yankin Bodo sun gurfanar da kamfanin a wata kotu ta Birtaniya inda kotun ta bada umarni ga kamfanin ya biya diyyar Fam miliyan 55 ga al'ummar wannan yanki da ke a yankin Niger Delta mai albarkatun man fetir.

Za a kuma rarraba kudin ne gida biyu Fam miliyan 35 za a raba tsakanin mutane 15,600 yayin da za a bada Fam miliyan 20 ga yankin nasu.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu