Shekaru 30 da kafa jam'iyyar CPDM a Kamaru | Labarai | DW | 24.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shekaru 30 da kafa jam'iyyar CPDM a Kamaru

Jam'iyyar Cameroon People's Democratic Movement ko CPDM da ke mulkin Kamaru na ci gaba da yin bukukuwanta na cika shekaru 30 da kafuwa.

An dai somo shagulgulan wannan biki ne daga birnin Maroua da ke arewacin kasar ta Kamaru, inda jiga-jigan jam'yiyyar suka yi ta bayyana irin nasarar da jam'iyyar ta samu ta samu a wadannan shekaru.

Sai dai jam'iyyun adawa a kasar sun ce al'umma ba su gani a kasa ba a wadannan shekarun da CPDM din ta yi tana mulki kana shugabanta Paul Biya aikata koma bai sai ma dai cigaba da kanankane madafun iko da ya ke yi.

Kamaru da ke da yawan mutane miliyan 21 na daga cikin kasahen Afirka da shugabanninsu suka shafe shekara da shekaru suna kan gadon mulki.