Shekaru 20 bayan kisan Ken Saro-Wiwa | Siyasa | DW | 10.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shekaru 20 bayan kisan Ken Saro-Wiwa

An cika shekaru 20 da yin hukuncin kisa kan Ken Saro-Wiwa, fitattcen dan gwagwamayar nan na yankin Niger da wasu mutane takwas na yankin Niger Delta a Najeriya.

Ken Saro-Wiwa dai marubuci kana dan gwagwarmaya ta kwato 'yancin yankin Niger Delda mai arzikin man fetur a Najeriya. A lokacin da ya ke fafutuka Saro-Wiwa kan shaidawa al'ummarsa ta kabilar Ogoni cewar ''za mu rikici da hukumomi amma fa ba da makamai ba. Za mu yi fada ne na masu ilimi kana za mu yi hakan ne cikin lumana don kada a zubar da jini.''

Nigeria Ogoniland Shell

An zargi kamfanin mai na Shell da gurbata muhalli a tarayyar Najeriya.

Da sanyin safiyar ranar 10 ga watan Nuwamban shekarata da 1995 ne dai aka rataye Saro-Wiwa da wasu mukarrabansa guda takwas bayan da wata kotun soja a lokacin mulki marigayi Janar Sani Abacha ta yanke musu hukuncin kisa saboda samunsu da hannu a kisan gillan shugabannin al'umma guda hudu. Kasashen duniya da jami'an diplomasiyya da kungiyoyin kare hakkin jama'a da Kungiyar Tarayyar Turai EU sun yi ta fama don a sassauta hukunci amma hakarsu ba ta kai ga cimma ruwa ba.

Kungiyar masu fafutukar kare yankin Ogoni ta MOSOP da ya ke jagoranta dai ta yi Allah wadai da yadda ayyukan hakar mai da kamfanoni ke yi a karkashin shell ke dada gurbata musu muhallai a yankin Niger Delta. A cewar Saro-Wiwa dai tun daga shekarata 1958 ne kamafanonin hakar man suka gurbata wannan yanki da suke kira "Aljannarsu a baya". Danyan mai da ke malala daga lalatattun bututun mai ya bata musu kasa wanda ya jawo talauci da barkewar cututtuka.

A kan haka ne kungiyar ta MOSOP ta nemi a gyara musu wuraren da aka lalata, tare da sanya al'ummar cikin gajiyar kudaden da ake samu daga hakar wannan albarkatu da ke yankinsu. Wadannan kudaden dai su ne kashi 90 daga cikin 100 da kasar ke samu wanda shugabannin kasar da mukarrabansu ke amfani dasu wajen cin karensu babu babbaka kamar yadda mazuna yankin suka yi zargi.

Ölverschmutzung im Ogoni NDelta

Malalar mai ta yi sanadin lalacewar muhalli a yankin Niger Delta

A ranar 4 ga watan janairu da aka yiwa lakabi ranar 'yan Ogoni, lokacin da kimanin mutane dubu 300 suka yi gangamin tunawa da ranar, gwamnatin mulkin soji a karkashin jagorancin Janar Sani Abacha ta mayar da martani da tura sojoji da suka mamaye yankin na Ogoni. An dakatar da zanga-zangar adawa da tsare Saro-Wiwa domin dadadawa masu kamfanin mai.

Hukuncin da aka yi wa Ken Saro-Wiwa da mukarrabansa takwas dai ya janyo korafi daga kasashen ketare. An yi yunkurin kakabawa Najeriya takunkunmi hana cinikin mai daga Amurka da wasu kasashen Turai amam abin bai yi tasiri ba, inda daga baya aka dakatar da kasar daga wakilci a kungiyar kasashen da Ingila ta rena wato Commonwealth, kana kanfanin Shell ya fice daga cikin yankin Ogoni.

Sauti da bidiyo akan labarin