Shekaru 10 na rikita-rikitar gina filin jirgin saman Berlin
Tun da aka fara aikin gina filin jirgin saman Berlin lamura suke tafiya a karkace. Akwai kuskure tun daga tsari da matsalar gini da tsaikon fara aiki da filin jirgin na tsawon shekaru. Wannan lamari ne mai muni.
Sharhi kan tsaikon da ake samu
An tsara budewa ranar 30 ga watan Oktobar 2011. Haka bai yuwu ba saboda kamfanin ya karye. Sau hudu ana sauya lokacin budewa. Abun kashe gobara ba ya aiki. Akwai lokacin da aka daina aiki bisa barazanar faduwar rufin. Yanzu ana fatan bude wajen zuwa karshen shekara ta 2017.
Babbar kasadar gobara
Duk da yake an yi amfani da tsauraran dokoki hukumar kashe gobara ta Jamus amma akwai gazawa a filin jirgin saman Berlin. Misali hanyoyin shan iska ba sa aiki sosai. Matsaloli sun faru ne tun daga masu zane. An nemi sauya wajen shan taba a kasa amma tilas sai an inganta.
Babbar waya
Idan ana magar kare lafiya babban abun damuwa shi ne hanyoyin wayoyi da suke cunkushe a sama. saboda fadada wuraren sauka kamfanoni sun kara hanyoyin wayoyi har zuwa lokacin da suka wuce kima. Haka ya zama hadari saboda galibi an yi cikin hanzari ba tare da cikekken bincike ba.
Na'urar haurawa da mutane sama ta tsuke
Yayin da wanda ya dawo daga tafiya kai tsaye zai tafi gida abin ya sha banban da wanda yake da kaya ya ke son sauka ya shiga jirgin kasa saboda tsukewar da ake da shi tsakanin hanyoyin. Haka hanyoyin bi da kaya sun banbanta da yadda aka tsara tun farko.
An dasa fiye da bishiyoyi 1000 na bogi
An shuka bishiyoyi 1036 na bogi. Dalili: mutumin da ya ke aikin ya sayo itatuwa wadanda ba su ake bukata ba yayin da aka tunbuke wasu bishiyoyin 600.
An tafka kurakurai wajen rubuta sunaye
An yi kuskure wajen rubuta suna na kashi daya bisa uku na dakuna 4000 da ke filin jirgin saman Berlin. Dalili: matsaloli na sadarwa. Zai yi wuya a sauya abu sannan a tuna abin da ya dace a rubuta. Wannan abu ne mai hadari saboda 'yan sanda da likitoci gami da masu kashe gobara wanda suke bukatar sanin dakin da za su je kai tsaye.
Abin da bala'i kan haifar
Zai iya zama filin jirgin sama mai jan hankali, sai abin da ake gani shi ne rashin lissafi daga tsari. Wannan babban aiki ya lakume kudaden da ware masa tun farko nunki biyu. A hukumance an samu kari zuwa Euro bilyan 5 da kusan rabi tun daga fara aiki da aka kiyasce zai lashe Euro bilyan biyu.
Koma baya da takardun bogi
An kai makura: tsohon daraktan kula da aiki na filin jirgin saman ya karbi cin hancin kimanin rabin milyan na kudin Euro. An daure shi sannan an gano babban mai kula da tsare-tsare ba shi da takardun aiki na injiniya mai kula da kariya, ya cancanta ne kawai da kula da aikin zane. Suka bisa rashin mutunta cancanta sun mamaye aikin.
Na gaba!
Wadanda suke da kula da aikin sun gaji da abin da yake faruwa. Cikin shekaru uku an sauya manajojin filin jirgin sama hudu. Hartmut Mehdorn (wanda yake hagu a hoto) a baya ya shugabancin hukumar kula da jiragen kasa. Majalisar dattawa da ke birnin Berlin ta kafa bincike kan wannan lamari kuma rahoton karshe ya nuna gaskiyar abin da ya faru.