Shekara guda rabon da ′yan matan Chibok su ga gida | Siyasa | DW | 14.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shekara guda rabon da 'yan matan Chibok su ga gida

Yau shekara daya kenan da ‘yan kungiyar Boko Haram suka sace ‘yan matan Chibok daga makarantarsu a jihar Borno kuma har yanzu babu labarin fiye da ‘yan mata 200.

Kwanaki 350 ke nan dai ‘ya'yan kungiyar ta Bring Back Our Girls suka dauka suna zaman dirshin a dandalin hadin kai da ke Abuja, inda suke rera salonsu na nuna fatar ta hanyar matsin lamba ga gwamnatin Najeriyar zata ceto ‘yan matan Chibok din su 219, wadanda aka sace su a daren ranar 14 ga watan Afrilun bara. Ko yaya masu gangamin na kungiyar Bring Back Our Girls ke ji shekara guda cur har yanzu ba labarin ‘yan matan na Chibok? Aisha Yesufu jigo ce a wannan kungiya

‘'To abin dai da ciwo da cin rai ace har an yi shekara guda ‘yan matan Chibok ba'a fito da su ba , duk da abubuwan da muka yi, mun fito mun fadawa gwamnati mun kai kukanmu mun shaidawa duniya baki daya, amma har yanzu ba'a fitar da ‘yan matan Chibok ba. Ni duk lokacin da na yi tuanni kwanaki 350 kenan muna fitowo amma ba'a dawo das u ba, sai inga Kaman ba'a samu nasara ba. Amma tunda mun dauki yaran nan Kaman ‘yayan da muka Haifa ne shi yasa har yanzu muke fitowa''

Nigeria Entführungen durch Boko Haram in Chibok

Duk da rashin tabbas, iyaye na kyakyawan zato

Ra'ayin iyayen 'yan matan

Ga iyayen ‘yan matan na Chibok dai har yanzu suna cikin hali na dimauta da damuwa, domin basu da tabs ko ‘yayan nasu suna a raye. Hauwa Abani na daga cikin iyayen ‘yan matan Chibok da aka sace su.

‘'Dole ne zuciya na ya baci, ‘yata da na yi wahala na dauka ciki kusan shekara na girmar da ita kuma ga kudin makaranta, a cikin noma wahala ne nike yi kafin in biya kudin amma kuma an zo an sace man ita, sannan ana man karya zaki samu yarinyarki , zaki samu yarinyarki amma karya ne. Ai tunda bata mutu na bizneta ba ko bayan shekaru 20 ne ina tsamanin zan ganta, bana fargabar cewa b azan ganta ba. Da ta mutu aid a an nuna man, ko bayan shekaru 20 ina sa ran wata rana zata dawo''.

Kyakyawar zato na sabuwar gwamnati

To sai dai ga Oby Ezekwesili shugabar kungiyar masu gangamin ganin an sako ‘yan matan ta Bring Back Our Girls ta ce zasu ci gaba da fafatawa har sai sun tabbatar da an dawo da ‘yan matan cikin koshin lafiya.

Nigeria Proteste Chibok Mädchen

'Yan kungiyar BringBackOurGirls sun ce ba za su yi kasa a gwiwa ba

‘'A matsayinmu na masu wannan gwagwarmaya mun dauki alakwari ga iyayen yaran nan tun da farko da muka yi magan das u, a lokacin da suka ce ba wanda ke kula da su ba mai magana a kan ‘yayansu. Saboda wannan alkawari koda mun fitar da fata sai mu sake samun kwarin guiwa da sabuwar fata. Gamu nan bayan shekara guda das ace ‘yan matan nan muna rike da yar kankanuwar fata, domin idab akwai rai to da rabo. Domin ‘yan matan nan suna nan a doron kasa, ba wai sun bace bane Kaman kumfar sabulu, don haka dole ne a ganon ‘yan matan nan''.

Zababben shugaban Najeriya Janar Muhammadu Buhari ya yi alkawarin kawo karshen aiyyukan ta'adanci a arewa maso gabashin Najeriya, musamman irin na Boko Haram da ked a alhakin sace ‘yan matan na Chibok. Ko yaya suke tunanen bullowa lamarin?

Duk da ganin sabuwar gwamnatin da ke jiran gado, masu gangamin sun yi imanin zasu ci gaba da matsin la,ba har sai sun ga komawar ‘yan matan Chibo gidajen iyayensu lafiya.

Sauti da bidiyo akan labarin