Shekara guda cikin halin kunci a Myanmar | BATUTUWA | DW | 01.02.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Shekara guda cikin halin kunci a Myanmar

Shekara guda ke nan da sojoji suka kifar da zababbiyar gwamnatin dimukuradiyya, a kasar Myanmar ko kuma Bama. Sai dai gwamnatin mulkin soja na fuskantar gagarumin kalubale na kin aminta da ita.

Zanga-zangar Myanmar | An rufe hanyoyi tare da hana taruka

Shekara guda ke nan al'ummar Myanmar ko Bama, na zanga-zangar adawa da sojoji

Tun dai bayan da sojojin kasar ta Myanmar ko Bama suka kwace mulki a ranar daya ga watan Fabarairun shekara ta 2021, dubban masu zanga-zanga da masu fafutuka da sojoji da masu adawa da sojojin ne suka halaka. Tabbacin adadin wadanda suka rasa rayukan nasu na da matukara wahala, kasancewar an dogara ne daga rahotannin da ake samu daga kungiyoyin kare hakkin dan Adam da har yanzu ke da katabus a kasar ta Myanmar ko Bama. Kungiyar kare hakkin dan Adam da ke adawa da mulkin soja ta kasar wato AAPP (Burma), ta nunar da cewa ya zuwa ranar 13 ga watan Janairun da ya gabata, kimanin mutane dubu daya da 463 ne suka halaka yayin da suke nuna adawarsu da juyin mulkin. Ita ma watwa kungiya mai zaman kanta mai suna (ACLED) ta kiyasata cewa kimanin mace-mace dubu 11 da ke da juyin mulkin aka samu a kasar ta Bama ko Myanmar, kuma an samu adadin ne ta la'akari da rahotanni da ake samu daga jaridu da kungiyoyi masu zaman kansu da kuma kafafen sada zumunta na zamani.

Jami'an tsaron Myanmar na amfani da karfi a kan masu zanga-zanga a Yangon

Jami'an tsaron Myanmar ko Bama, na murkushe masu zanga-zanga da karfin tuwo


Wani rahoto da kungiyar kwadago ta duniya ta fitar a watwan Janairun da ya gabata dai, ya nunar da cewa kimanin mutane miliyan daya da dubu 600 ne suka rasa ayyukansu tun bayan juyin mulkin sojojin. Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, kusan mutane dubu 350 sun tsere daga gidajensu yayin da ake ci gaba da halaka 'yan jarida ko kuma kama su ko suka fice daga kasar domin tsira da rayuwarsu. A tsawon shekarun da suka gabata dai, mafi yawan lokuta rikici na afkuwa ne tsakanin rundunar sojojin kasar. A yanzu dai ana gwabza kazamin fada a manyan jihohin kasar ta Bama. Nuna tirjiya ga sojojin da ke bazuwa dai, ya samo asali ne bayan gagarumar zanga-zangar adawa da juyin mulkin sojan a kasa baki daya ta gaza tilastawa gwamnatin sojan sauka daga madafun iko. Sojojin sun samu nasarar fatattakar masu zanga-zangar daga kan tituna ta hanyar amfani da karfin tuwo, abin da ke janyo asarar rayukan fararen hula.. Sai dai amfani da karfin, ya haifar da karuwar nuna kyama ga gwamnatin mulkin sojojin. Koda yake babu cikakken rahoto, amma masu sanya idanu sun nunar da cewa mafi yawan al'ummar kasar ta Myanmar ko Bama ba su amince da gwamnatin mulkin sojan ba.

Sauti da bidiyo akan labarin