1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Rohingya sun bijire wa komawa gida

Zainab Mohammed Abubakar MA
August 23, 2019

Sabon yunkuri na mayar da rukunin farko na 'yan gudun hijirar Rohingya zuwa Myanmar ya ci tura. Hukumomin Bangladash inda suke fakewa sun tabbatar da hakan.

https://p.dw.com/p/3ONtf
Rohingyas Flüchtlinge kehren nach Myanmar zurück
'Yan gudun hijiran Rohingya a BangaladeshHoto: DW/A. Islam

A 'yan kwanakinnan ne dai ma'aikatan majalisar Dinkin Dubniya suka kai ziyara sansanin talakawa 'yan gudun hijira na 'yan Rohingya, da ke Cox Bazar da zummar neman wadanda za su yarda a sake mayar da su kasarsu ta asali Myanmar. Akwai sunayen mutane dubu uku a kan takardar da ke hannunsu, na rukunin 'yan gudun hijirar da za'a iya komarwa gida, wadanda hukumomin Bangladash da na Myanmar suka yi hadin gwiwar tantancewa. Sabbir Ahmed wani dottijo da ke sansanin ya ce ya gwammace mutuwa, kamar yadda da yawa suka fuskanta a kasar da suka baro.

Musulmi 'yan Rohingya wajen dubu 700 aka tilasta wa barin matsugunansu a kakar shekara ta 2017, walau saboda gudun tsira da rai daga rikicin da ya barke, ko kuma daga dakarun tsaron kasar da suka afka musu. Tun daga wancan lokacin ne dai 'yan gudun hijirar ke tsugunne a kasar Bangladash da ke makwabtaka.

Bangladesch Angelina Jolie besucht Rohingya-Camp
Wasu jami'an agaji na duniya a BangaladeshHoto: Getty Images/AFP

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin agaji na duniya kamar Caritas na kasar Jamus da kungiyar agaji ta Deutscland hilf", da ke tallafa musu, sun sha yin gargadi dangane da yunkurin mayar da 'yan gudun hijirar.

 

Su ma dai 'yan gudun hijirar abun da suke hange ke nan idan har gwamnatin Myanmar ba za ta yi la'akari da 'yan Rohingya a matsayin 'yan kasa da takardun izinin kasancewa 'yan kasa ba, shakka babu, ba ranar komawa a cewar dan gudun hijira Sayedul Haque.

A yanzu haka dai sabon rikici ya sake barkewa tsakanin sojojin Myanmar da dakarun 'yan awaren Arakan da ke jihar Rakhine. Kuma rahotanni na nuni da cewar kamar yadda ya kasance da 'yan Rohingya, a yanzu ma wannan rikicin ya haifar da cin zarafin bil adama, batu da gwamnatin Myanmar din ta ki yin komai a kai.