Shaye-shayen miyagun kwayoyi | Zamantakewa | DW | 16.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Shaye-shayen miyagun kwayoyi

Matsalar shaye-shaye tsakanin matasa tana kara fadada cikin kasashen masu tasowa kamar Najeriya.

Matsalar Safara da shaye-shayen miyagun kwayoyi matsala ce da ke mayar da hannun agogo baya a kokarin da ake na tsabtace halayyar al'umma. Babban abin damuwa a yau shi ne yanda makarantun gaba da sakandare matsalar ta samu gindin zama inda matasa suka tsunduma kansu cikin harkokin shaye-shaye.

Masu lura da al'amura dai na ganin har su kansu yan siyasar zamani na taimakawa ga lalata matasa ta fannin shaye-shaye, abin da babban jami'in kula da yaki da shan miyagun kwayoyi ya gaskata.

Iyaye da dama suna masu bayyana takaicin yadda 'ya'yansu kan ari wata tarbiya ta daban sakamakon miyagun abokanai. Madam Azura Senci Bawa ta sashen kula da masu shaye-shaye da ke a harabar NDLEA a Sokoto ta yi bayani yadda suke fama da mashaya. Wannan dai matsala ce da ke bukatar kulawar kowa a tsakanin al'umma.