Shawarwarin karbar Turkiyya a KTT | Siyasa | DW | 30.09.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shawarwarin karbar Turkiyya a KTT

A ranar uku ga watan oktoba ake so a fara shawarwarin karbar Turkiyya a KTT

Kasar Austriya ce ummal’aba’isin mawuyacin halin da aka shiga inda ta dage akan cewar lalle sai an shigar da manufar nan ta kawancen alfarma, a matsayin zabi akan ba wa Turkiyya cikakken wakilci a Kungiyar ta Tarayyar Turai. Ita kuma Turkiyya ta ce faufau ba zata yarda da haka ba. A lokacin taronsu na gaggawa, a ranar lahadi mai zuwa ake sa ran ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar zasu kawar da sauran abubuwan dake hana ruwa gudu domin fara shawarwarin karbar Turkiyyar, wacce jami’an siyasarta a halin yanzu suke bayyana dari-dari da kuma takaicinsu a game da take-taken kungiyar. A misalin watanni uku da suka wuce kusan dukkan kasashen KTT suka shiga biki da murnar cewar a daidai ranar uku ga wata za a fara shawarwarin karbar Turkiyya. Amma ga alamu a yanzu murna neman komawa ciki sakamakon matsalolin dake neman su hana ruwa gudu bisa manufa. Da farko dai an fuskanci matsala daga kasashen Faransa da Cyprus kuma a yanzu sai ga kasar Austriya na neman saka ayar tambaya a game da ainifin makasudin tattaunawar karbar kasar ta Turkiyya. Ba tare da wata rufa-rufa ba ministan harkokin wajen Turkiyya Gül ya bayyana takaicinsa a game da wannan drama ta ‚ya’yan kungiyar a Brussels, inda ya ce za a fuskanci matsaloli masu yawan gaske. Kuma muddin kasashen kungiyar ba su tantance ainifin makasudin shawarwarin ba to kuwa ba shi ba halartar shagulgulan gabatar da su a ranar uku ga watan oktoba. A dai halin da muke ciki yanzu ministan harkokin wajen na Turkiyya ba zai zarce kai tsaye zuwa Brussels ba, zai dakata ya saurari sakamakon taron na gaggawa na ministocin harkokin wajen kasashen Kungiyar ta Tarayyar Turai da kasar Austriya ta ba da shawarar gudanarwa. Gül ya ce:

2. O-Ton Gül

„Es gibt Dinge…

Akwai wasu abubuwa, wadamnda har abada kasar Turkiyya ba zata lamunta da su ba, kuma dukkan kasashen Kungiyar Tarayyar turai sun san da haka.

Manufar ministan harkokin wajen Turkiyyar a nan shi ne kasancewar kasar ta hakura da gaskiyar cewa shawarwari zasu dauki shekaru masu yawa ana gudanar da su ba tare da an tsayar da wata takamaimiyar manufa ba. Amma fa bai kamata kasashen na Turai su yi watsi da gaskiyar cewa manufar shawarwarin ce a kai ga karbar Turkiyya a matsayin cikakkiyar wakiliya a kungiyar ba. Bugu da kari kuma Turkiyya ba zata yarda da wani sabon sharadi ba. A dai halin da ake ciki yanzun, hatta Turkawa dake sha’awar manufofin kasashen Turai sun fara kosawa da lamarin kuma muddin aka ci gaba da yi wa Turkiyya matsin kaimi har tura ta kai bango mai yiwuwa kasar tayi watsi da manufar ma gaba daya, in ji ministan harkokin wajenta.