Shariar EFCC a Nigeria | Labarai | DW | 16.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shariar EFCC a Nigeria

A yaune aka saurari shariar tsoffin gwamnoni uku a tarayyar Nigeria,wadan hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin Nigeriar zagon kasa,ta EFCC ta shigar gaban daya daga cikin manyan kotuna kasar dake Abuja.

Gwamnonin da suka hadar dana Jihohin Jigawa,Saminu Turaki da na Plateau,Joshua Dariye da kuma Uzor kalu Orji ,dai basu samu beli kamar yadda suka nema a yau din ba.

EFCC dai na zargin Tsohon gwamnan jihar Jigawan da wasu kampanoni 3 da wani mutun,da sama da fadi da kimanin Naira dubu 56,Mutuminda kuma kotun ta bada umurnin tafiya dashi Kurkuku,Ayayinda Joshua Dariye da ake zargi da laifuffuka 14,aka bada umurnin barinshi a hannun hukumar ta EFCC.