Sharhi: Jiya iyau a nadin ministoci a Najeriya | BATUTUWA | DW | 24.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Sharhi: Jiya iyau a nadin ministoci a Najeriya

Daga yanayin mutanen da shugaban ya zaba da ma yawansu da kuma irin matakan da aka bi wajen zabarsu ya barranta da irin abin ya rika fadi a lokacin yakin neman zabe

Shugaba Buhari dai ya shafe watanni biyu bayan kama aiki a wa'adinsa na biyu ba tare da girka gwamnati ba amma wannan tsaiko da aka samu ya kare a ranar Talata bayan da ya fidda sunayen mutane 43 da yake son yin aiki tare da su a matsayin ministoci. Wasu daga cikin mutanen dai fitattun 'yan siyasa ne yayin da wasu kuma ba su yi fice na a zo a gani ba a fagen siyasar wannan zamani. Har wa yau akwai wasu daga cikinsu da za a iya cewa shugaban ya yi hangen nesa wajen yanke shawarar yin aiki da su duba da irin kwazon da suka nuna a ire-iren aiyyukan da suka yi a baya.

Nigeria Amtseinführung Boss Gida Mustapha (DW/U. Musa)

Boss Mustapha sakataren gwamnatin Najeriya

Wani abin dubawa kuma shi ne yadda ya bi doka sau da kafa wajen fidda minista guda daga kowacce jiha kamar yadda sashe na 147 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya shardanta, sai dai ba a nan gizo yake sakar ba domin baya ga minista guda da kowacce jiha ta rabauta da shi, shugaban ya kewaya sassan kasar shidda inda nan ma ya fidda mutum guda wanda zai wakilici sashen. Duk da dai hakan bai saba ka'ida ba idan aka yi la'akari da sashi na 147 sakin layi na daya na kundin tsarin mulkin kasar, amma gwamnatin da ke son takaita kashe kudi ba gaira ba sabar bai kyautu a ce ta yi haka ba sai dai kuma idan irin wannan yunkuri a fatar baki kawai yake.

Shekarun mutanen da shugaban ya zaba a matsayin ministoci ma dai abin dubawa ne domin mutum zai iya kidaye yawan wandanda suke kasa da shekaru 50 da yatsun hannunsa, hasalima dai mafi kankantar shekaru a cikinsu shi ne mai 45 wanda a tsari na kasa da kasa ba za a kira dan shekaru 45 matashi ba. Wannan ya saba da irin alkawuran da shugaban ya yi musamman a lokacin yakin neman zabe na damawa da matasa kuma ko ma ba wannan alkawari kyautuwa ya yi a ce an dubi irin yawan matasan da kasar ke da su da irin rawar da suka taka a lokacin zaben da ya ba shi nasara wajen saka musu da alheri ta hanyar sanya kwararru daga cikinsu a gwamnatinsa.

Nigeria Präsidentschaftswahlen Frauen Wahllokal (picture-alliance/AP Photo/S. Alamba)

Mata a kan layi lokacin zabe a Najeriya

Yawan matan da shugaban ya sanya cikin jerin ministocinsa za a iya cewa ya saba da irin abin da ya rika fada a baya na baiwa iyaye mata dama ta baje kolin irin kwarewar da suke da ita. Sanya mata 7 a cikin gwamnatin da ke da yawan mutane 43 za a iya cewa an yi ba a yi ba idan aka yi la'akari da irin rawar da suka taka wajen zabe da kuma yadda kasashen duniya ciki har da wasu na nahiyar Afirka ke yi. Misali a nan shi ne kasar Habasha da a baya-bayan nan ta baiwa mata kashi 50 cikin 100 na mukaman minista a gwamnatin Firaminista Abiy Ahmed.

Baya ga batun dan zubin da aka yi wa mata a sabuwar majalisar ministocin, akwai wasu daga cikin mutanen da aka mika sunayensu duk kuwa da zarginsu da ake yi na sama da fadi da dukiyar kasa lokacin da suke rike da mukamai a baya har ma a lokuta da dama wasunsu suka shiga komar hukumar EFCC da ke yaki da masu irin wannan halayya. Ga shugaban da ke da'awar yaki da cin hanci har ma hakan ya zama jigo na yakin neman zabensa tun daga ranar da ya shiga sabgogin siyasa kawo yau bai kamata a ce irin wadannan mutanen na rabarsa ba har ma ya kai ga amincewa da su ya basu mukamai.

Yanzu dai da yake shugaban ya yi nasa, shawara ta rage ga 'yan majalisar dattawan kasar da ke da wuka da nama wajen tantance ministoci, da su tuna irin hakkin da ya rataya a wuyansu na al'ummar da suke wakilta wajen yin abin da zai ciyar da su gaba maimakon farantawa shugaban kasa. Hanya daya rak da za su yi hakan ita ce ta zaben mutane masu amana da hazaka da kwarewa wajen gudanar da aiki

Sauti da bidiyo akan labarin