Shakku kan sahihancin yarjejeniya da B/Haram | Siyasa | DW | 08.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shakku kan sahihancin yarjejeniya da B/Haram

Yayinda kwamitin da gwamnatin Najeriya ta kafa domin nemo hanyar yin sulhu tare da yin afuwa ga 'yan kungiyar Boko Haram yace ya cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, mazauna arewa maso gabashin kasar sun bayyana shakkunsu

Yawancin al'ummar yankin arewa maso gabashin Najeriya inda nan ne rikicin da ake dangantawa da kungiyar nan mai fafutukar kafa shari'ar musulunci a Najeriya da aka fi sani da Boko Haram ya fi kamari, na bayyana shakku kan sanarwa musamman ganin daga bangaren gwamnati ta fito.

Da yawa na ganin matukar ba Imam Abubakar Shekau, shugaban wannan kungiya ne ya bayyana matsayin bangaren su ba, ba mai amincewa da wannan sanarwa, ganin a baya ma anyi irin wannan sanarwa amma ba abinda ya biyo baya. Adamu Adamu mai Dala, wani mai bibiyar yadda al'amuran tsaro ke tafiya ne a Najeriya.

Duk da wannan sanarwa kuma, rahotanni na nuna cewa babu bangaren da ya ajiye makami, inda jami'an tsaron suka yi ikirarin hallaka ‘yan kungiyar gwagwarmayar sama da arba'in a garin Maiduguri. Haka kuma a karshen makon nan wasu ‘yan bindiga da ake zaton ‘yan kungiyar gwagwarmayar ne suka hallaka wasu dalibai da dama a wata makarantar Sakandare dake Mamudo a yankin Potiskum a jihar Yobe.

Nigeria Terror Leiter der Terrorgruppe Boko Haram Sektenführer Imam Abubakar Shekau

Kakakin kungiyar Boko Haram Imam Abubakar Shekau

Bisa la'akkari da irin hare-haren da ake kaiwa a wannan yanki da ke ci gaba da lamushe rayukan al'umma yasa al'ummomin yankin suke bayyana shakku kan shiri na tsagaita wuta wanda kuma ta bangaren gwamnati kawai ya fito. Garba Tela Herwa Gana Gombe,wani mai fafutukar kare hakkin talakawa ne a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Wasu dai kamar Malam Ibrahim Wazana na ganin abinda ke hana ruwa gudu dangane neman kashe wutar wannan rikici shine akwai masu cin moriyar sa. Na tambaya Malam Zakari Adamu, shugaban rundunar adalci ta jihar Yobe wanda yayi tafiyar kusan kilimita 100 don samun hanyar sadarwa, kan me ya kamata gwamnati tayi domin mutane su yarda da shirin tsagaita wutar sai ya ce.

“…… Abinda gwamnati ta fada ya tabbata cewa an gani a kasa ba kamar irin maganganun baya ba a fada ya wuce to duk mutumin da ka gaya masa magana ya duba ya ga ba haka bane, gobe ka gaya masa ya ba haka bane to koda zaka da gaskiyar gobe zai yi dar-dar ba zai taba yadda ya baka amana ba sai wannan abin ya tabbata gaskiya ne…….”

Anschlag Nigeria Sekte Boko Haram

Farautar 'ya'yan kungiyar Boko Haram

Gwamnan jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya ya yi kira ga gwamnatin tarayya gami da jami'an sojoji da su saki layukan wayoyin waya da aka katse sanadiyyar dokar ta baci da shugaban Najeriya ya kafa a jihohin Adamawa da Borno da Yobe. Gwamnan dai ya bayyana cewa sakin hanyoyin sadarwar shine zai baiwa jama'a damar taimakawa jami'an tsaro, tare da bada misali da yadda mutane suka ga wadanda suka kai hari a makarantar garin Mamudo amma ba bu yadda za su iya sanarwa jami'an tsaro saboda matsalar rashin hanyoyin sadarwa.

Mawallafi: Al Amin Suleiman Mohammad
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin