1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Dage shari'ar Nnamdi Kanu

Abdoulaye Mamane Amadou LMJ
July 26, 2021

A Najeriya kotun da ke sauraron shari'ar madugun 'yan awaren Biafra Nnamdi Kanu ta dage zaman shari'ar tasa har zuwa watan Oktobar wannan shekara, sakamakon hutun da alkalai suka shiga.

https://p.dw.com/p/3y4eW
Nigeria Biafra Separatist Nnamdi Kanu
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Kotun karkashin mai shari'a Binta Nyako ta bayyana hutun alkalan da ke farawa a wannan litinin din a daukacin Najeriyar, a matsayin hujjar dage shari'ar da ta dauki hankali. To sai dai kuma ba a iya gabatar da Kanu a gaban kotun ba, duk da cincirindo na magoya baya da kuma 'yan kungiyar IPOB da suka je kotun domin kallon yadda take shirin kayawa. A cikin watan Yunin da ya gabata ne dai, aka damke Kanu a kasar Kenya tare da iza keyarsa zuwa Abuja.

Cincirindon magoya bayan dan fafutukar sun ce suna fatan ganin adalci kan jagoran nasu, kamar yadda Ngozi Patrick da ke zaman daya a cikin magoya bayan Kanun ta shaidawa wakilimu a Abuja Ubale Musa. A gefe guda kuma ana sa ran gurfanar da Sunday Igboho a gaban kuliya a wannan Litinin din a binrin Cotonou na Jamhuriyar Benin, bayan kama dan fafutukar rajin kafa kasar Yarabawa ta Oduduwa a yayin da yake kokarin tserewa zuwa Jamus a tsakiyar wannan wata na Yuli.