1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saukowar farashin kaya a Najeriya

August 16, 2019

An fara samun saukin hauhawan farashin kaya a bana a Najeriya

https://p.dw.com/p/3O2f3
Flash-Galerie MC Lagos Marktfrau
Hoto: DW

A ci gaba da neman mafita ga tattalin arzikin tarrayar Najeriya da ya fada cikin wani hali a shekaru hudu, ofishin kiddidiga na kasar ya ce kasar na samun raguwar hauhawan farashin kaya a shekarar bana ta 2019.

Wata sabuwar kiddidiga daga offishin kiddiga na tarrayar ta Najeriya ta ce a cikin watanni goma sha biyun da suka gabata hauhawar farashi na raguwa a cikin kasar da ke neman mafita ga matsin tattalin arziki.
A watan Yulin da ya shude kidddidiga kan farashin ya ragu zuwa kaso 11.1 maimakon kaso 11.4 da yake a watan Yuni.
Farashin abinci, da ke kan gaba a cikin hajjar ciniki ta kasar, a fadar sabuwar kiddigar ya ragu daga kaso 13.6 a watan Yunin zuwa 13.4, cikin watan da ya shude. 
Duk da cewar dai har yanzu kasar ba ta yi nasarar maida hauhawar zuwa tsakanin kaso 6 zuwa tara a cikin dari da ke zaman babban burin bankin CBN ba, ana kallon ci gaban raguwar, a matsayin alamu na daidaiton lamura ga kasar da a baya ta kalli hauhawar da ta haura kaso 20 cikin dari.
Tuni dai dama babban bankin CBN din ya fitar da sabon umarnin hana biyan kudin ruwa kan duk wasu kudaden ajiyar da suka kai Naira Miliyan Dubu Biyu a bankuna da nufin hana tashin farashi da kuma walwalar kudi a hannun al'umma.
A baya dai masu arzikin tarrayar Najeriya kan zabi ajiye kudi a asusun ajiya na lokaci mai nisa da nufin samun riba, maimakon juya su da gina hanyoyin cigaba ga tattalin arzikin da har yanzu ke neman komawa daidai tun bayan masassara ta shekara ta 2016.
To sai dai kuma a fadar Abubakar Ali da ke zaman wani masani na tattalin arzikin tarrayar Najeriyar, saukar ta farashi ba tana nufin ci gaba ba, musamman ma cikin halin rashin kudin da ke a aljihun 'yan kasar.
A cikin wannan mako ne dai shugaban kasar ya baiwa bankin umarnin tsaida bada kudade na waje da nufin sayo kowane nau'i na abinci zuwa cikin kasar a wani abun da ake yiwa kallon yunkurin kara bunkasa kasuwar cikin gida da kila ma rage kudaden waje.
To sai dai kuma akwai tsoron matakin na iya kaiwa ga hauhawa in har kasar ta fuskanci karancin bukatun kayyakin abincin.
Amma  kuma a tunanin Yusha'u Aliyu da ke zaman mai sharhi ga tattalin arzikin tarrayar Najeriyar, na iya fadawa a cikin sabon tsari na kasuwar bai daya ta nahiyar Afirka a wajen biyan bukata ta abincin in har ta kama.

A yanzu dai Najeriya na fatan ci da kanta, abin da ke zama wani sabon nuna kwazo a kokarin magance matsalolin kasar don kawo karshen tashin hankalin da ke ta ruruwa cikin kasar a halin yanzu, tare da dora batun tattalin arzikinta kan tudun muntsira.

Nigeria - Abuja tomato market
Hoto: DW/S.Olukoya
Nigeria | Markt in Kaduna
Hoto: DW/Z. Umar