1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya za ta wajabta rigakafin corona

Abdul-raheem Hassan
May 19, 2021

Rigakafin cutar corona zai zama izinin shiga ma'aikatu da hukumomin gwamnati da motocin haya a Saudiyya daga ranar 1 ga watan Agustan 2021.

https://p.dw.com/p/3taUd
BG Coronavirus Impfung rund um die Welt | Saudi-Arabien Riad
Hoto: Ahmed Yosri/REUTERS

Dokar za ta shafi ma'aikatu masu zaman kansu da wuraren motsa jiki da makarantu, kowa sai ya nuna shedar yin rigakafin kafin ya samu damar shiga. Sabbin dokokin na zuwa ne kwanaki kalilan bayan da hukumomin Saudiyyar suka umarci ma'aikatan da suka yi rigakafin ne kadai za su komawa bakin aiki.

Bayan shafe shekara guda ba wanda yake fita wajen Saudiyya, yanzu gwamnati ta dage takunkumin hana fita kasashen ketere ga wadanda suka yi rigakafin. Yayin da kasar ta ba da sharudan yin rigakafin ga maniyyata da ke son sauke faralin aikin hajjin bana.