Saudiyya za ta sayi jiragen yaki a Jamus | Labarai | DW | 03.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saudiyya za ta sayi jiragen yaki a Jamus

Kasar Saudiyya na shirin sayan jiragen ruwan yaki a hannun Jamus

Wasu kafofin watsa labaran Jamus sun ruwaito cewa kasar Saudiyya na shirin sayan jirgin ruwa na yaki a hannun hukumomin Jamus. Bisa ga bayanan da jaridar "Bild am Sonntag" da ake bugawa a ranar Lahadi anan tarayyar Jamus ta wallafa dai, jirgin ya na daya daga cikin biyar da take da niyan saye a kan tsabar kudi miliyan dubu biyu da 500 na Euro. Hakazalika kasar ta Saudiyya ta tsara sayen jiragen ruwa na yaki guda 25 a nan tarayyar Jamus a cikin shekaru masu zuwa.

Sai dai wannan batun na sayar wa Saudiyya da makamai, ya jawo kace nace tsakanin jam'iyyar CDU ta Angela Merkel da kuma wacce take zawarci da nufin kafa gwamnatin hadaka wato SPD. Dama dai sayar wa kasashe da ke da hannu a cikin yake yaken da makamai, ya na daga cikin al'amuran da suka kawo tseiko a kokarin kafa gwamnati da ake yi tsakanin bangarorin biyu. Jam'iyyar Social Demokrat na neman a tsaurara wannan doka. Ana zargin Saudiyya da mara wa 'yan tawayen Siriya baya a kokarin da suke yi na hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita. Saleh Umar Saleh