Saudiyya za ta kara farashin man fetur | Labarai | DW | 28.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saudiyya za ta kara farashin man fetur

Hukumomin Saudi Arabiya sun bayyana cewar za su yi karin kashi 40 zuwa 50 cikin 100 na farashin man fetur da 'yan kasar ke saye daga ranar Talata (29.12.15) idan Allah ya kaimu.

Kamfanin dillancin labarai kasar na SPA ya ce majalisar ministocin kasar karkashin jagorancin Sarki Salman ne ta amince da karin wanda baya ga man na fetur da wannan karin zai shafa, za su yi kari kan farashin abubuwa da suka hada da ruwan sha da wutar lantarki da man kananzir.

Majalisar ta ce ta dau wannan matakin ne saboda yadda farashin makamshi yanzu haka ya kasance a kasuwannin duniya. Wannan na zuwa ne bayan da kasar ta bayyana cewar za ta fuskanci gibin kasafin kudi na kimanin dala biliyan 90 a kasafin kudi na 2016.