Saudiyya ta shirya wa aikin hajjin bana | Labarai | DW | 29.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saudiyya ta shirya wa aikin hajjin bana

Mahukunat kasar Saudiyya sun sanar a wannan Talata da cewa sun dauki matakin tunkarar duk wata matsala da ka iya tasowa a lokacin aikin hajji bana

Mahukunat kasar Saudiyya sun sanar a wannan Talata da cewa sun dauki matakin tunkarar duk wata matsala da ka iya tasowa a lokacin aikin hajji bana wanda zai samu halartar mutane sama da miliyan biyu daga kasashen Musulmi daban-daban na duniya. A wata fira da manema labarai a wannan Talata, kakakin ministan cikin gida na kasar ta Saudiyya Mansour Turki ya ce daga cikin mutane miliyan biyu da za su halarci aikin hajjin na bana dubu 200 'yan kasar ta Saudiyya ne.