Saudiyya na yada wahabiyanci a duniya | Labarai | DW | 10.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saudiyya na yada wahabiyanci a duniya

Wani rahoto da wata cibiyar kwararru a Birtaniya ta fitar ya nuna kasar Saudiyya na kan gaba wajen yada akidar wahabiyanci a kasashen duniya.

Wani bincike da wata cibiyar kwararru ta Henry Jackson a Birtaniya ta fitar ya nuna kasar Saudiyya na taka muhimmiyar rawa wajen yada tsattsauran akida a  tsakanin musulmi.

Bayan mummunan harin ta'addanci a Birtaniya, masana sun gudanar da bincike daban daban kan abin da ke haddasa tsattsauran akida. Kwararrun masana a kungiyar Henry Jackson sun wallafa nazarin da suka yi na binciken hanyoyin samun kudade ga masu tsattsauran akida a Birtaniya, an kuma gano cewa kasar Saudiyya, ita ce akan gaba wajen bada gudunmawa.

Rahoton yace a shekaru 50 da suka gabata, Saudiyya ta zuba akalla dala biliyan 86 wajen yada akidar Wahabiyanci da ke zama tushen tsattsauran akida na kungiyoyin jihadi a duniya baki daya.

Susanne Scröter daraktar cibiyar bincike ta addinin Islama dake Frankfurt a nan Jamus ta bayani da cewa  

" Ta ce ban yi mamaki da wannan binicke ba. Saudiyya ta dade tana yada akidar wahabiyanci wanda yana da kamanni da akidar yan IS tare kuma da yada farfaganda, ta na kuma aikewa da kudade ga masallatai da makarantu domin yada akidar ta wahabiyanci ga al'umma."