Sallah bikin daya rana. | Zamantakewa | DW | 24.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Sallah bikin daya rana.

A jamhuriyar Nijer tamkar wasu yankuna na Najeriya da Boko Haram ta addaba an yi bukukuwan sallah cikin matakai na tsaro.

Eid Al Fitr in Zinder, Niger

Masallata a filin idi a Nijer

A yankunan jahohin da ke a gabashi da suka hada da Damagaram da Diffa ma dai kamar sauran sassa na jamhuriyar Nijer hawan idin babbar sallar ya wakanan salim alim inda kuma aka samu halartar dubban jama'a Musulmi inda bayan sallah raka'a biyu tare da Fatiha nan take aka yanka ragon liman kafin daga bisani sauran al'umma su yanka tasu layyar.

Sallah cikin rashin kudi

Niger Agadez Afrika

Al'umma na duba dabbobin sallah

Sultan na Damagaram Abubacar Sanda ya yi barka da salla ga jama’arsa. Sallar dai ta bana tazo cikin wani yanayi na rashin kudi ga mafi yawan jama’a, kamar dai a yankin na Damagaram haka abun yake a jihar Diffa mai fama da rikicin Boko Haram banbanci guda ne anan jama'a har suka kamalla salla jirgin yaki na shawagi a kan su.

Interfaith Mediation Centre in Kaduna

Mabiya addinin Kirista da Musulmi a lokacin ziyarar juna

Ziyarar Kirista wajen Musulmi

A can Kadunan Najeriya kuwa wata tawagar limaman coci-coci sanye da manyan malun-malun sun kai ziyarar barka da sallah ga takwarorinsu malaman addinin musulunci da sauran al‘umma Musulmai, don kara kulla dankon zumunci da kawar da kyamatar juna. A Jihar Adamawa da ke daya daga cikin jihohin da rigimar ta Boko Haram ta shafa, ko shakka babu dai, ana iya cewa sallar layyar bana, ta zarta ta bara dama shekarun da suka gabata ta fuskar natsuwa tsakanin masallata dama wadanda ke makwabta idan aka danganta da yadda fargaba ke mamaye bikin a shekarunda suka gabata. Al’umma sun yi sallah cikin matakan tsaro yadda ya kamata.