1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saliyo: Zaben shugaban kasa zagaye na biyu

Suleiman Babayo
March 30, 2018

A wannan Asabar din (31.03.2018) al'ummar kasar Saliyo za su yi zaben shugaban kasa zagaye na biyu domin tantance wanda zai jagoranci kasar nan gaba.

https://p.dw.com/p/2vFuy
Wahlen in Sierra Leone
Hoto: DW/Abu-Bakarr Jalloh

Kimanin masu zabe milyan 3.1 da ke kasar ta Saliyo a yankin yammacin Afirka za su tantance wanda zai dauki madafun iko tsakanin jagoran 'yan adawa Julius Maada Bio na babbar jam'iyyar adawa ta SLPP da kuma Samura Kamara na jam'iyyar APC mai mulki. Tun farko an jinkirta zaben da aka tsara zagaye na biyun tun ranar Talata sakamakaon wani hukuncin kotu amma yanzu an kammala shirye-shirye domin zaben.

Masu sanya idanu ciki kuwa har da tsohon Shugaba Goodluck Jonathan sun nuna gamsuwarsu da yadda shirin ke tafiya inda ya ke cewar "na gamsu da abubuwan da na gani zuwa yanzu domin demokaradiyya ta na aiki kuma zan yi amfani da wannan dama domin neman 'yan kasar Saliyo su fito kamar yadda suka yi a zagayen farko domin zaben mutumin da zai shugaban kasar na gaba.

Ita dai kasar ta Saliyo a baya ta yi fama da yakin basasa na fiye da shekaru 10 lamarin da ya kai ga mutuwar dubban mutane. Baya ga wannan kasar ta yi fama da annobar cutar nan ta Ebola mai saurin hallaka mutane inda kimanin mutane 4000 suka rasa rayukansu. Kasar har wa yau ta fuskanci ibtila'i na zabtarewar kasa da aka samu a shekarar da ta gabata ta birnin Freetown inda fiye da mutane 400 suka rasu. Domin haka zaben na wannan Asabar na zama zakaran gwajin dafi kan samar da cigaba a kasar ta Saliyo.