Saliyo: Addu′oi ga wadanda zaftarewar kasa ta halaka | Labarai | DW | 20.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saliyo: Addu'oi ga wadanda zaftarewar kasa ta halaka

A wannan Lahadin, mujami'u a sassan kasar Saliyo sun gudanar da addu'oi na musanman don wadanda bala'in zaftarewar kasa ya halaka a makon da ya gabata.

A wannan Lahadin, mujami'u a sassan kasar Saliyo sun gudanar da addu'oi na musanman don wadanda bala'in zaftarewar kasa ya halaka, mutane fiye da dari hudu ne suka mutu a wannan iftala'in a yayin da wasu dari shida suka bata, yanzu haka akwai daruruwan mutane da suka rasa matsuguninsu, kungiyoyin agaji na ci gaba da bayyana fargabarsu dangane da yiwuwar barkewar cututtuka, wannan kuma ya biyo bayan karancin ruwa mai tsabta da kasar ke fuskanta bayan ibtala'in zabtarewar kasa sanadiyar ruwan sama mai karfi.

Ganin yawan wadanda suka rasa matsuguni ya sa yanzu Kungiyoyin agajin ke kokarin ganin ba'a sami barkewar cuta ba, kungiyoyin na kokarin rarraba abun tace ruwan sha a fadin birnin na Freetown don kaucewa barkewar cututtuka da ke da nasaba da gurbataccen ruwa.