Sakwato: Matashi mai yin dorin kariyar kashi | Himma dai Matasa | DW | 30.01.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Sakwato: Matashi mai yin dorin kariyar kashi

Wani matashi da ya kammala digirinsa a jami’a ya jingine kwalin digirinsa ya kuma rungumi sana’ar gyaran wadanda suka samu kariya ko kuma tazgade a kasuwannin Jihar Sakkwato .

Nigeria Bombenanschlag in Gombe (picture-alliance/dpa)

Wannan tsohon hoto ne da aka dauka a Gombe a asibitin masu jinya muka yi amfani da shi

Matashin dai Umar Isa da ya kammala digirinsa a fannin lafiya bangaren gwaje-gwaje da kuma aune-aunen jini a  can jami’ar Ahamadu Bello da ke Zariya ya bayyana cewa dama dai ita wannan sana’a  ya gajeta ne tun iyaye da kuma kakanni kuma ya soma ne tun yana dan kimanin shekaru takwas. To amma sai dai Umar ya ce ya yanke shawarar rungumar sana’ar ne bayan da mahaifinsa ya umurceshi da ka da ya soma aikin gwamnatin ya bar hanyar taimakon da yake yi wa al’umma lamarin da yanzu ya kaishi yawon wannan sana’a a ciki da wajen Najeriya.

Sauti da bidiyo akan labarin