1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Matakin gwamnati zai taimaki ilimi?

Uwais Abubakar Idris LMJ
January 13, 2026

Gwamnatin Najeriya ta amince da sabon tsarin sake amfani da takardun karatun da aka yi amfani da su, a daukacin makarantun firamare da na sakandire a kasar.

https://p.dw.com/p/56m1i
Najeriya | Makarantu | Dalibai | Littattafan Karatu
Najeriya ta umurci sake amfani da littattafan karatun da aka yi amfani da su ga dalibaiHoto: Alemnew Mekonnen/DW

A wani mataki na samar da sauki ga iyayin yara da ma bunkasa samar da ilimi da a shekarun nan ke fusknatar kalubale a kasar ne, gwamnatin Najeriyar ta ce a rinka sake amfani da littattafan karatun a makarantun boko. Sabon tsari ne fil da gwamnatin Najeriyar ta bullo da shi a kokarin samar da sauki ga ilimin boko da ma alkinta muhalli, saboda amincewa da sake amfani da litattafan karatun da aka yi amfani da su a makarantun firame da na sakandiren, zai taimaka a dawo da ingancin karatu da na kayan koyarwa a Najeriyar.

Iyayen yara za su samu sauki?

Iyayen yara a Najeriyar sun dade suna fuskantar tasku, saboda dan karen tsadar da karatun bokon ke da shi a kasar. A kowane zangon karatu ya zama dole a sayi sababbin litattafai ga dalibai, kasa yin hakan kan tilasta wasu dalibai daina zuwa makaranta, abin da ke kawo cikas ga ilimin boko, a kasar da ke da kimanin yara kanana sama da miliyan 18, wadanda ba sa zuwa makaranta.

Soshiyal midiya na cikin dalilan faduwa WAEC na 2025

Sababbin tsare-tsaren da ma'aikatar kula da harkokin ilimi ta Najeriyar ta bullo da su, sun hadar da samar da tsarin karatu na bai daya a makarantaun firamare da sakandire na kasar, domin kara yi saita karatun bokon kasar da kuma hana duk wani biki na karshen shekara da a kan tilasta iyayen yara tara kudi domin yinsa. A yanzu gwamnati ta ce sai yaran da ke shekarar karshe ta karatun karamar sakandire da wadanda za su kamala ne kawai, aka amince su yi irin wadannan bukukuwa.

Kalubalen iyaye a makarantu masu zaman kansu

Koda yake makarantun gwamnatin Najeriya na samar da ilimi kyauta, a matakin firame zuwa shekaru uku na sakandire. Sai dai makarantu masu zaman kansu na kan gaba wajen matsawa a kan biyan kudin sababbin litattafai da kuma kin amincewa da sake amfani da litattafan karatu. Aiwatar da wadanan sauye-sauye muhimmi ne a tsarin karatun boko na Najeriyar da yake matukar bukatar samun canjin da zai zaburar da shi, ta yadda zai zo daidai da zamanin da ake ciki.